DON MATA (BIREDI)

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu. Yan uwa mata yau gani dauke da wani nau’i na kayan fulawa mai saukin sarrafawa, mai matukar daukan hankali a ido,  mai sanya mai gida hadiyar yawu tun kan a kai baka,  mai dadin dandano da saukin tauna.
     Uhmmm, wata kila uwargida ta ce wai shin wannan wane irin nau’in kayan fulawa ne mai sanya zumudi. Kar ki damu ki biyoni sannu cikin dakin girki idonki ya gane miki.😊
     Uwargida ki tanadi wadannan kayan kamar haka:

Fulawa gwangwanin madara 4 
Sugar rabin(1/2) gwangwani
KWAI guda 1
Gishiri  1/2 tsp
Yeast 1 tbs
Banana flavor 1 tsp
Vanila flavor 1 tsp
Man gyada 4 tbs
Madaran ruwa 1/2 gwangwani
Ridi dan daidai.

Alhamdulillah, bayan uwargida ta tanadi duk abinda ake bukata. Sai ta samu baho ko kwanonta mai tsafta madaidaici.
YANDA AKE KWABAWA
Ana bukatar uwargida ta tankade fulawar a cikin abinda za ta yi kwabin, sai ta zuba YEAST da GISHIRI ta gauraya, sai ta dan yi rami a tsakiya ta sa MAN GYADA, FLAVORS, KWAI da ruwa dan madaidaici. Sai ta kwaba, kwabin ya zama kamar na fanke amma ya dan fi na fanke tauri.
In ta gama sai ta rufe sosai ta kai shi rana na tsawon minti 40 ko awa guda zata ga ya hau. (Idon kuma uwargida tana so ya kumbura shap shap sai ta dafa ruwan zafi ba Lallai sai ya tafasa ba, sai ta juye a babban baho ta sa kwanon da kullin ke ciki. Ba zai dau lokaci ba nan da nan zai kumbura). Daga nan sai ta samu inda take murza cin-cin ta barbada fulawa ta juye kullin akai ta dada kwaba shi. Sai ta baza shi yayi fadi amma da dan tudu kar yayi fale-fale. (Ba ki bukatar abin murza fulawa hanu ma ya wadatar tunda ba tauri). Ana bukatar uwargida tayi amfani da cookies cutter, amma idon babu tana iya amfani da bakin kofi. Tana yi tana jerawa akan tire bayan ta barbada fukawa a kan tiren gudun kamawa. Idon ta gama yankawa sai ta shafe kai da madara(na ruwa) sai ta barbada Ridi akai, ta bar shi ya dan kara kumburi kamar haka.

image

Toh uwargida daga nan sai ki koma wajen Oven dinki. Kin san dama Biredi gasa ta ake. Sai ki hau gashi. Amma don Allah uwargida a kula kar a bari ya kone.
Ya kamata ya fito kamar Haka
image

Um um yaya ki ka gani? kar a bari ya huce. Maza a hada abin sha a isa ga mai gida. Nasan ya kosa, don kin ciki nasa ciki da kamshi tuni.

Bissalam sai mun hadu a kwabi na gaba.

             

Advertisements

2 Comments

Add yours →

  1. Masha Allah. Jazakh Allahu khair. Muna jiran more mouth watering delicacies

  2. Masha Allah bless you

Please Comment

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s

%d bloggers like this: