GODIYA GODIYA GODIYA

Alhamdulillah wassalatu wassalamu ala man la nabiyya ba’adahu. Godiya ta tabbata ga Ubangijin al’arshi. Sarkin da ba kamar Sa, mai kowa mai komai. Mamallakin sammai da kassai.
   Ya Ubangiji ina rokon Ka kasancewar Kai kadai ba ka da abokin tarayya. Wanda bai Haifa ba, ba a haife Shi ba, Ya Allah Ka shiryar da ni in Zamo daga masu godiya zuwa gareka. In za ma mai godewa ni’imarka.
   Ya Allah Kai Ka yi umurni ga duk wani musulmi mai iko da ya ziyarci Dakinka mai girma da daukaka. Ya Allah na amsa kira, na Kai ziyara, na samu ikon yin ibada a Masallatan da suka fi kowane masallaci daraja a duniya.
   Ya Allah abubuwa da yawa Sun faru, na tsoro da firgici da tashin hankali. Wanda hakan bai kasance ba sai da sanen Ka. Ya Allah Ka sanya hakan Ya za mo wani Rahama ga yan uwanmu da suka rasa rayuwarsu yayin gudanar da wannan ibada. Allah Ka sa Ya zamo Aya garemu mu da muke tare da su da kuma sauran musulmai baki daya.
   Godiya da yabo gareka ba za su taba karewa gareni ba. Ina rokonka da Ka da ka nuna min wani rana a rayuwata da zan nuna gajiyawa da godiya gareka. Hakika zuwa aikin Hajja ibada ne, domin ya na daya daga cikin cika ciken musulunci guda biyar. Sai dai kuma duk wanda zai tafi, yana kudurtawa ne a ranshi cewan ko Ya dawo ko ba zai dawo ba Ya tafi kenan.
   Shiyasa duk wanda zai tafi za ka same shi ya na mai neman gafarar mutane, ya na fadin Allah ya kaddara saduwa. Lallai ko abin haka Ya ke. Domin wani in ya tafi Ya tafi kenan ba zai sake dawowa ba. Sallamar da ya yi da iyaali da yan uwa da abokan arziki Shi ne ya ke zama abin tunawa garesu.
   Wannan shine abinda ya faru da yan uwa musulmai wadanda muka yi wannan tafiya mai dinbin albarka tare da su. Ya Allah ka karbi shahadarsu. Allah Ka sanya Jannatul firdausi Ya zamo masaukin su a gidan AlJannah. Ameen.
   Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Ina kara godiya ga
Allah subhanahu wata’ala da ya kaddare ni da dawowa cikin iyali na. Allah ka bawa wanda bai Je ba ikon zuwa. Ya Allah ka ba ni iko in kara Kai ziraya.
   Rabbana ta kabbal minnaa innaka antas sami’ul  aliym. Wa tub alayna innaka antat tauwaabur rahim.

Advertisements

Please Comment

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s

%d bloggers like this: