RIBAR FADIN GASKIYA

A’uuzu billahi minash-shaydanir-rajiym. Bismillahir-rahmanir-rahiym. Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Ubangijin talikai. Mai Kowa mai komai. Mamallakin sammai da kassai. Ubangijin Al-arshi. Mai cikekken iko akan bayinsa. Wanda ya yi umurni da aikata mai Kyau. Kuma ya ke hani da aikata mummuna.
     Yaa ku wadanda ku ka yi Imani (wadanda kuka bada gaskiya) ku ji tsoron Allah matukar Jin tsoron shi, (gargadi gareku) kada ku kuskura ku mutu face Kuma masu mika wuya, ma’ana kuna musulmai.
     Ya yan Uwa Musulmai, inai mana sallama da sallama irin ta addinin musulunci. Assalamu Alaikum warahmatullahi wa barakatuhu. Amma ba’ad:
     Yau gani dauke da wata tunatarwa ga yan Uwa. Aya ce na dauko cikin Qur’ani mai girma Daga suratul Ahzab aya ta saba’in. In da Allah S. W. T ke cewa: “ياأيها الذين آمنوا اتقوا الله و قولوا قولا سديدا”
“ma’anar ayar itace “Ya ku wadanda ku ka yi Imani, ku zama masu tsoron Allah, Kuma masu fadin gaskiya”. Ya yan Uwa, idon muka dubi ayar da Kyau duba da idon basira duba na hankali zamu ga cewa Ubangiji mai girma da daukaka ya na umurtan bayinsa amma ma su imanin cikin su da su kasance ma su tsoron Shi. Masu yin abinda ya ce, kuma masu barin abinda ya hana. Haka zalika Su kasance masu bauta mi Shi cikin tsakanin tsoron shi kamar suna ganin shi gabansu. Kamar yanda ya zo cikin hadisi, lokacin da Mala’ika Jibril (A.S) ya tambayi Shugaban talikai game da IHSAN (KYAUTATAWA) Annabi (S. A.W) ya ce: ” IHSAN shine ka bautawa Allah. Kamar ka na ganin Shi. Idon kai baka ganin Shi, to shi yana ganinka.
         Ma’ana kai mai imani ka ji tsoron Ubangijinka a duk inda ka ke, ka sani jin tsoron Allah shine ginshikin zaman lafiyar ka. Duk zuciyar da bata da tsoron Allah hakika ta zama rubebbiyar zuciya, ba kyakkyawa cikinta sai mummuna, haka kuma ba alkhairi cikinta sai sharri. Wa’iyazubillah. Allah ka tsare mu daga zuciyar da ba Imani.
        A karshen ayar Ubangiji madaukakin sarki ya yi umurni kuma ya gargade mu da mu kasance masu fadan gaskiya. Ma’ana kada mai Imani ya yarda wani kalma ya fito daga bakinshi face abinda Allah ya yarda da shi. Ubangiji bai yarda da karya ba don haka bai son mai karya. Da wannan na ke Jan hankalin yan uwa musulmai ma Su imana da mu yi koyi da fadar Manzo (s.a.w) inda ya ce: “Duk wanda yai imani da Allah da ranar karshe to ya fadi alkhairi ko yai shiru”.
        Ubangiji madaukin sarki mai Rahma ne, kuma mai jin kai. A duk lokacin da yai umurni to tabbas akwai romo ko garabasa ga duk Wanda ya bi kuma ya aikata abinda aka umurce shi da yi. Kamar yanda ya zo cikin wannan ayar da na ke bayani a kai. Allah SWT ya yi wa mumunai alkawari cewa duk Wadanda suka bi to ga abinda zasu samu. “Zai shirya da Ku, Ku zama masu aikata ayyuka na kwarai; kuma har wa yau garabasa ta biyu ” Zai yafe muku zunubanku”.
         Ya Kai dan/Yar uwa me yafi wannan dadi? Allah ya yafe muku laifukanku da suka wuce, wadanda kuka aikata cikin sani ko rashin sani. Haka kuma dangane da zunuban da za Ku yi nan gaba Allah zai taimakeku Ku zama masu tuba daga garesu. Banda Allah wa zai mana wannan kyautan.
        Me muke da shi, da me muka dogara da har Allah mai girma da daukaka zai bada umurni mu ce ba za mu bi ba? Duk wani abu da Ubangiji ya ce ayi to ribarshi na mu ne.
        Abinda na fada dai dai Allah ya bani ladanshi abinda nai kuskure Ina rokon Allah ya yafemini.
        Rabbana ta qabbal Minna innaka anta’s sami’ul alim. Wa tub alaina innaka antat tauwabur rahim. Subhana rabbuka rabbil izzati ammaa yasifun wassalamun alal mursalina walhamdulillahi rabbil aalamin.

Advertisements

Please Comment

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s

%d bloggers like this: