DON MATA ()

Assalamu alaikum warahmatullahi wa barakatuhu ya ‘yan uwana Mata. Sai yau Allahu ya nufe ni da isa kusa da buhun Fulawa na. Kamar yanda nai alkawarin koyadda abubuwa da ake sarrafa su da Fulawa. To yau gani dauke da abu mai sauki wajen sarrafawa, Kuma mara nauyi wajen hadiya. Haka zalika Kuma marar cinye albashin mai gida.
      DA farko dai Uwargida ki tanadi wadannan kayan hadin:
Fulawa gwangwa 4
Man gyada tbs 5
Gishiri 1/2 tsp
Yeast tbs 1
Madaran(gari) tbs 2
Kwai guda 1
Sai ruwa da Kuma man suya.

             Yanda ake kwabawa
    Uwargida ki samu kwanonki mai tsafta Sai ki tankade fulawar a ciki, Sai ki kawo Yeast, gishiri, sugar, da madara ki zuba akai ki cakuda su. In kin tabbatar sun gaurayu Sai ki buda tsakiya ki zuba man gyada, ku fasa kwan ki zuba Sai ki sa ruwa Dan daidai (Nasan dai Uwargida baza ta fara wannan aiki ba Sai ta tsaftace hanunta) Don Haka Sai Kawai ki sa hanu ki fara kwabawa. Ana so Kwabin ya zama Kamar irin na meat pie. (ba tauri ba, ba ruwa ruwa ba).
     Idon ya kwabu to ba a bari ya jima, Sai Kawai ki fara mulmulawa. Za ki gutsetstsira su yan kanana ba Kuma can sosai ba. Sai ki mulmula ko wanne Kamar ball. Kafin nan ki tanadi tire ki shafeshi da mai Don Kar ya kama. Sai ki rika jerawa, amma ki rika barin sarari tsakanin su, don gudun hadewa idon sun kumbura. Idon kin gama Sai ki samo abu ki rufe ko ki zira tiren cikin leda. Ki bar shi ya yi Kamar awa daya. Sai ki duba, in kin ga ya tashi Kamar haka:
       

image

Toh anan Sai Uwargida ta dora man suyarta a wuta ta fara suya. Ga yanda ya ke idon an soya.
           

image

☺ Uwargida ya kika gani? Ya burge ko? To Don Allah a cire kiwa a dage a jarraba.
        Karin bayani, kina iya dafa kwai Sai ki raba daya zuwa biyu, inkinzo mulmula fulawar Sai ki Dan buda tsakiya ki sa kwan ki rufe. Kamar yanda ake buns. Don Allah a cire amaja ake yiwa mai gida ya na Ci da shayi.
   Idon akwai abinda Uwargida bata gane ba, Don Allah a yi tambaya. Farin ciki na ne in ga ‘yar uwa ta mace na sarrafa Fulawa cikin korewa.
            Bissalam. Sai mun hadu a kwabi na gaba.

Advertisements

One Comment

Add yours →

  1. madinatu tukur May 13, 2015 — 9:37 pm

    Malam khadija Allah ya saka maki da alkhairi da wannan aiki na tunatarwa da kike yi.ya kuma sa ya zama sadakatul jariya a gareki.ya shirya maki zuria.
    Don Allah malama akwai wani abu dake ciman tuwo a kwarya da nakeso kiyi mana sharri a akai.watau yanda aure ya zama a kasar hausa.yanzu sai kiga in zaa auras da diya mace iyayenta ne tamkar keyin komi.zaa basu empty gida duk su cika shi da alatu.to maras hali fa.kuma yana kawo rashin bama maijin girma daga matar.
    na biyu wanda kuma yafi damuna watau shagalin bukin.da kayan da ake sawa.wasu ma tamkar rigar auren xtians suke sawa.a yamutse maza da mata abun kunya hadda iyaye maza da mata ana rawar banza.
    wannan ai saba wa ubangiji Allah ne sosai.inaga yana cikin dalilin da yasa aurenma baya albarka.

Please Comment

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s

%d bloggers like this: