DON MATA

   Assalamu alaikum ya ‘yan uwa Mata.  Too…. Yau gani dauke da sabon rubutu, amma ba iron na kullum ba. Nasiha ta ta yau ta raja’a ne akan ‘yan uwana Mata. Haka kuma hannunka Mai sanda ne ga ‘yan uwa maza.
   Dalili na na fadin haka shine, don su suke wahala idon ba su yi dace ba, ko in ce idon idanuwan su suka rufe wajen lura da muhimman abubuwa wadanda suke taka muhimmiyar rawa a bangaren zamantakewa.
    A hakikanin gaskiya abubuwa da Dama idon aka rasa su a zamantakewan cikin Gida na ma’aurata, hakan na matukar taka rawa wajen rugujewar farin ciki da walwala tsakanin ma’aurata.
   Don haka na kudiri a niyyar taimakawa ‘yan uwana mata ta hanyar tunatar da su muhimmamcin  farin cikin mai gida. Watakila ‘Yar uwa ta ce shin wadanne abubuwa ne wadanda na da mu da fadin ce wa su  na sanya Mai gida farin ciki da walwala? Haka ne, idon kina tare da ni Ina magana ne akan Iya sarrafa abinci. Domin shine kashin bayan walwalan Mai Gida cikin gidan shi, Kai tare ma da daga Kai da hura hanci cikin abokai, ta hanyar nuna allfahri.
   To… ‘Yar uwa, idon ba kya adawa da FULAWA, ki biyo ni sannu a hankali za ki ga yanda FULAWA za ta sha kashi(wuya) a hanuna. Idon kuma  na yi rashin sa’a ke ba ma’abociyar mu’amala da FULAWA ba ce. To Ina rokonki da ki daure ki Ara mana lokacinki, da nutsuwarki, da hankalinki, tare da juriya DA hakurinki wajen biyoni cikin kwabe- kwabe na. Ina Mai tabbatar Miki sai kin zo ke ma kina koyar da su.
   DA fatan za ki biyoni sannu a hankali don  koyan abinda zai sanya Mai Gida daga Kai tare da karsashi. Allah ya sa mu da ce. Ameen

Advertisements

Please Comment

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s

%d bloggers like this: