TSORON ALLAH

Wassalatu wassalamu ala man la Nabiyya ba’adah. Assalamu alaikum ya ayyuhal ikhwan.
Nasiha tagaremu a Yau itace TSORON ALLAH. A hakikanin gaskiya a zamanin da muke ciki a Yau, ba abinda mafi yawa daga cikin mutane suka Rasa ko in CE yai karanci cikin al’umma kamar TSORON ALLAH.
Da alama mafi yawan mutane suna mantawa cewan Allah AL BASIRUN ne, ma’ana maigani ne, Wanda ganin Shi ya buwayi ko Ina, haka kuma babu abinda yake boye masa.
Ya Kai Dan Adam, dai na yaudarar kanka kana Shiga waje kana aikata barka, a gurbacecceyar tunaninka ka buya daga jama’a. Shin ka manta Allah Yana ko Ina Kuma Yana ganin duk abinda bawa ke aikatawa walau a bayyane ko a boye?
Shin kana tunanin kana da mabuyar da zaka aikata barka ba tare da Allah masanin gaibu ya ganka ba?
Shin kana ko tunawa da wani rana mai zuwa Wanda zaka tsaya gaban ubangiji ka karanta abinda ka aikata da bakinka?
In tuna maka ya Kai Dan uwa musulmi. Shin ka manta da azaba da fitinar cikin Kabari, Wanda ke jiran duk Wanda ya je Mata Yana mai sabawa Allah da Manzonsa saboda rashin tsoron Ubangiji?
Kai! Dan uwa musulmi, tashi kafarka idon ma barci kake. Ka sani cewa jin tsoron Allah shine ginshiki na kasancewarka cikekken musulmi. Tsoron Allah ne kadai zai kaika inda bayin Allah na kwarai su ka kai.
Shin me yai maka dadi a rayuwa Wanda ka biye Mata har kake aikata Sabo ba tare da jin tsoron gamuwarka da Ubangijinka ba?
Ya Kai Dan Uwa! Ka sani CE wa Manzon Allah Wanda akai duniya dominsa kuma fiyayyan halitta wanda ba wani mai matsayi wajen Ubangiji duk duniya kamarsa. Amma Yana tsananin tsoron ubangijin Sa. Asalima ba Wanda ya Kai shi tsoron Allah.
Shi yasa Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya umurcemu da muyi koyi da shi. Kamar yanda ya zo a cikin Hadisi inda yake cewa “ITTAQILLAHA HAITHU MA KUNTA”. Ma’ana ka ji tsoron Allah a duk in da ka ke.
idon muka dauki fadakarwan da ke cikin wannan hadisin to tabbas da mutum ya kyautatawa rayuwarsa. Ya na da kyau a kullum mutum ya Rika rokon Allah ya Kara masa tsoronSa.
Tsoron Allah kuma baya samuwa har sai in mutum ya FI karfin zuciyarsa. Idon da tsoron Allah shaidan ba zai Yi nasara a kanka ba, balle har ka sabawa Ubangijinka.
A karshe nake cewa mu ji tsoron Allah domin shine mafi cancanta da a ji tsoro. Abin takaici sai ka samu wani Yana bala’in jn tsoron Dan uwansa Dan Adam, Yana gudun bacin ran Sa. Amma kash…… Baya tsoron Mahaliccinsa.
Ya Allah Ina rokonKa da ka shiryar da mu zuwa ga yawaita tsoronKa. tsoronka.Kasanyamu

Advertisements

Please Comment

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s