MUTUWA

Duk kan yabo da godiya sun tabbata ga Allah madaukakin sarki. Ubangijin Al’arshi. Tunatarwa ta Yau gareku ya ‘yan uwa musulmi ita CE Mutuwa. Wayyo! Ko a fadin sunar akwai firgitarwa. Wai shin menene abin firgitarwa ga wannan sunan? Na san wasu za su Yi wannan tambayar. Duk Wanda ya san akwai Rayuwa to tabbas ya san akwai mutuwa. Saboda ba lallai bane ya budi ido ya ga kakan kakanshi, in ko haka ne to tabbas yasan wataran shi ma zai bi su. Ashe mutuwa ita CE kishiyar Rayuwa. Kamar yanda haske yake kishiyar duhu. Don haka Yana da kyau mu san ma’anarta, da kuma alakarta da Dan Adam.
Wato ita dai wannan kalma ta MUTUWA ta na nufin Datsewa, ko sandatarre abinda baya motsi. Idon aka datse Abu to an tsaida shi ne daga motsi. Ya zama Mara amfani ya zama macecce tunda baya motsi.
Ita kuma mutuwar masana sun CE iri biyu CE. Akwai babba(mai yanke jin dadi) akwai kuma ta Hutu wato na jin dadi. In an CE mutuwar jin dadi Ana nufin mutuwar barci. Allah ya Yi dare ne don bawa ya huta, Hutu kuma ya na zuwa ne a cikin Barci. Shi kuma Duk Wanda ya kwanta barci to bashi da Mara ba da matacce. Tun da baya sanin halin da ya ke ciki. Idon Allah ya so, kuma kwanan mutum bai Kare ba, sai Allah (S.W.T) ya dawo masa da rayuwarsa. Don haka malam Bahaushe ke CE wa “Barci kanin Mutuwa”.
Idon kuma kwana ya Kare, sai ya zarce zuwa ga babban Wanda in an tafi ba dawowa. Shikenan, rayuwa ta kare, al’amura sun tsaya, babu kuma sauran motsi.
Mutuwa kenan, mai Mai da Mata zawarawa, mai mai da yara marayu. Mai yanke jin dadi, mai raba masoya. Mutuwa mai kashe birane, mai raya makabarta. Ya Kai dan Adam shin ka tanadi wajen buya idon ta zo? Tunda ba makawa sai ta zo, al’amarine Wanda zai faru a rayuwar Dan Adam. Bai zo ba, bai wuce ba, ba kuma zai fasa zuwa ba. Duk kan mai rai Mutum ko Aljan, har da dabbobi duk bazasu tsira ba, kowa sai ya dandane ta. Da akwai Wanda Allah zai tsirar ya wuce lahira ba tare da ya dandaneta ba, da Allah (S.W.T) ya tsirar da manzonsa. A Aha! Ta kofarta kadai ake wucewa aje Lahira.
Ya Kai Dan Uwa shin ka na tune da wannan rana? Wane tanadi Kai Mata? Manzon Allah (S.A.W) ya horemu da mu nemi tsari daga fitinar Rayuwa da fitinar Mutuwa. Ashe mutuwa abar tsoro CE.
Ya Allah! Ka Yi mana Rahma, ka ba mu Sa’ar tafiya, ka Sa mu cika da kyau da Imani. Ya Allah! Kar ka kashe mu face muna Musulmi ma su cikakkun Imani. Ameeen

Advertisements

5 Comments

Add yours →

  1. May Allah swa reward u dis sadaqatul jari enlightening us, stay blessed

  2. Allah yasa idantaxomana mucika da imani domin annabin rahama (s a w )

Please Comment

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s

%d bloggers like this: