FALALAR ZHIKRI

A’uzubillahi minash-shaidani rajim. Bismillahir- Rahmanir-Rahim. Godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki mai kowa mai komai.
Yau ga ni gareku da wani sako amma ba sako na nishadantarwa ba, sako ne na tunatarwa. Na san da yawa daga cikinmu sun Sa ni, sai dai Kawai in tunatar da Su, domin shi Dan Adam Allah ya Yi shi mai yawan mantuwa da gafala. To a Yau Ina so in tunatar da mu ga me da muhimmanci da kuma falalar ambaton Allah(zhikri). Abu ne mai sauki amma mai wuyar aikatawa ga Wanda bai san falalar shi ba.
Yawan falala, da lada, da gafara da ke cikinta, Allah da kan Shi ya sha fada cikin Qur’ani cewan a ambace Shi. Domin yin hakan akwai riba ga Dan Adam. Kamar yanda Allah ya ce cikin suratul Baqara aya ta 152 “Ku ambace ni Zan ambace ku, ku gode mini kada ku butulce mini”.
Allah (S.W.T) Yana son bawa ya gode mi shi, duk da godiyar ba zai Kara wa Allah komai ba. Sannan ya CE cikin suratul Ahzab aya ta 41 ” Ya ku wadanda Su ka Yi Imani ku ambaci Allah ambato mai yawa”.
Ya Kai Dan uwa musulmi, tsarkake bakinka ta hanyar ambaton Allah da sunayensa kyawawa. Mu lizimci yin azhkar safe da maraice. Domin yin hakan zai Kare mu daga munanan abubuwa.
Duk mai yawaita Yin azhkar zai za mo cikin kariyar Ubangiji. Allah madaukaki zai za mo mai tafiyar da rayuwar shi. Haka kuma zai Sa mu nitsuwar zuciya. Ya na daga cikin falalar zikiri duk gidan da ake yin ta to ma zauna ciki za Su za ma masu samun nitsuwa da kariya daga Allah. Haka kuma aljanu baza Su Shiga gidan ba. Sannan zai kare mutum daga sharrin mugayen mutane.
Ya Yan uwa musulmai! Mu nemi littafin Husnil Muslim, ba mu ajiye a ma’ajiya mai kyau don mun iya ajiya ba. A’a, so nake mu lizimci karantata, duk wani zhikri da ake nema ya na ciki.
A karshe na ke cewa kada mu sake hidimar Duniya ta dauke mana hankali mu shagala ga barin ambaton Allah. Mu dubi hidama da dawainiya da Sahabban Manzo (S.A.W) suka Yi wa Musulunci. Amma hakan bai shagaltar da Su ba. An samo daga sahabin Manzo (S.A.W) ya CE da Manzon Allah ” Ya Ma’aikin Allah shari’o’in musulunci sun Yi yawa a gare ni, saboda haka ka nuna mini wani Abu da Zan Yi riko da shi. Sai Ma’aikin Allah yace da shi “Kar harshenka ya gushe face Yana Danye daga ambaton Allah”.
Ya Kai Dan uwa wane aiki gareka da baza ka ambaci Ubangijinka ba dare da Rana?

Advertisements

Please Comment

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s

%d bloggers like this: